Jihohi uku na Kudancin Sudan da ma babban birnin yankin sun kada kuri’ar neman ‘yancin kai da gagarumar rinjaye, bisa ga daftarin sakamakon da aka bayar yau Laraba.
Masu shirya zaben raba gardamar a babban birnin Kudancin kasar Juba sun ce kashi 97.5 cikin dari na masu kada kuri’a a wurin sun zabi ballewa ne daga Arewaci.
Jami’ai sun ce fiye da kashi 90 cikin dari na masu kada kuri’a a sun zabi ballewa a Jihohin Unity, da Lakes da Yammacin Bahr al-Ghazal na Kudancin kasar.
Ana sauraron cikakkun sakamako a sauran jihohi bakwai, kuma dole sai an tantance dukkannin kuri’u a hukumance.
Miliyoyin ‘yan Kudancin Sudan ne dai su ka kada kuri’unsu a zaben raba gardama kan batun ballewarsu daga Arewacin Sudan. Yankunan sun yi yakin basasa na tsawon shekaru 21 wanda ya zo karshe a 2005.
Masu sa ido na kasa da kasa sun bayyana zaben raba gardamar da cewa babu rufa-rufa, kuma babu tursasawa kuma anyi adalci ciki.
Za a bayyana sakamakon wuccin gadi a hukumance ran 31 ga watan Janairu. Ana sa ran samun cikakken sakamako ran 14 ga watan Fabrairu.
Wani jami’in Jam’iyyar National Congress mai mulkin Arewacin Sudan ya ce ya na kyautata zaton Kudancin zai zama ‘yantacciyar kasa da zarar an tabbatar da sakamakon a hukumance.
Rabi Abdelati Obeid ya gaya wa sashen Turanci na Muryar Amurka, Shiyyar Afirka a yau dinnan Laraba cewa, a shirye Jam’iyyar NCP ta ke ta amince da sakamakon zaben, ko da kuwa na ballewa ne.
Obied ya kuma ce ya yi imanin cewa irin yadda jam’iyyarsa ta dukufa wajen ganin an gudanar da zaben yadda ya kamata ya isa ya gamsar da gwamnatin Amurka karkashin Barack Obama ta cika alkawarinta na maida huldar jakadanci da Sudan, tare da cire sunan Sudan daga jerin sunayen kasashen da ke yada ta’addanci.