Da aka fara tsayar da ranar mata a nan Amurka matan sun soma ne da yin zanga zanga a birnin New York suna neman a biyasu albashi daidai da maza tare da basu 'yancin yin zabe da tsayawa zabe.
Abubuwa sun soma daidaita a nan Amurka saboda an warware batun albashi muddin mace tana da ilimi daidai da namuji a wurin aiki. Tuni suka samu 'yancin shiga yin zabe da tsayawa takara.
Saidai a rana irin ta yau mata sukan yi nazari ne kan inda suke yanzu su duba ko har yanzu a wannan kasa dake ikirarin tana ba kowa 'yanci akwai abubuwan da har yanzu an hanasu ko kuma ana takura masu.
Amurka bata nuna banbanci tsakanin jinsi. Mace da namuji suna da 'yanci daya da haki daya. Babu banbanci tsakaninsu. Babu nuna wariya tsakanin mace da namuji. Darajarsu daya kuma dole ne a basu matsayi daya ko a gaban shari'a.
Top saidai duk da cewa yau shekaru fiye da dari ke nan da tsayar da ranar mata tare da daidaita hakinsu da na maza amma har yanzu ana nuna wa mata wariya da banbanci a wasu kasashe da dama a duk fadin duniya. Haka ma akan ganawa 'yan mata azaba tare da cin zarafinsu a wasu kasashen.
Dangane da batun mata Amurka ta ciga matuka tun zanga zangar farko akan 'yancin mata a shekarar 1908. A nan Amurka mata sun samu 'yancin yin zabe ko kuma shiga takara. A cikin ma'aikata sun kwashe kimanin rabi, wato suna daidai da maza. Yawancinsu nada digiri daga jami'o'i kamar yadda maza suke dasu. Suna karbar albashi mai tsoka.
Amma duk da cigaban da Amurka ta samu akan 'yancin mata ita ce kasa ta 28 cikin 145, wato har yanzu akwai kasashe 27 dake gabanta da suka fi kula da hakkokin mata.
To ko yaya lamarin yake a kasashen Afirka? Zamu duba kasashe biyu.