Sakamakon zaben ya nuna cewa jamiyyar ta Aung San Suu Kyi na National League for Democracy ita ce ta lashe zaben da tazara.
Fadar White House tace shugaba Obama ya kira ita Aung san Suu Kyi domin yaba mata da irin kokarin ta wajen sadaukar da kai na tsawon shekaru da dama domin ganin an samu zaman lafiya da ingantaciyyar demokaradiyya a kasar ta Mayanmar wato Burma.
Haka kuma shugaba Obama ya lura cewa wannan zaben tare da samar da sabuwar gwamnati wani babban mataki ne da zai ciyar da kasar ta Burma gaba musammam ma akan harkokin demokaradiyya tare da inganta zaman lafiya.
Har wayau shugaba Obaman ya kira shugaban kasar na Myanmar, Shugaba Thein Sein inda ya nuna masa muhimmacin mutunta sakamakon zaben wanda shine ra'ayin yan kasar Burma.
Sai dai kuma Fadar ta White House tace har yanzu akwai bukatar ganin an yi wasu gyare-gyare a cikin dokar kasar wanda hakan zai iya baiwa ita Aung SAN Suu Kyi damar zamowa shugabar kasar.