Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A guji jinin wanda ya yi balaguro zuwa inda cutar Zika ta bulla - WHO


Margaret Chan, shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO
Margaret Chan, shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO

Hukumar kiwon Lafiya ta duniya mai lakabin W.H.O. ta baiwa jami'an kiwon lafiya umurnin kada su karbi gudumawa jini daga mutane da suka yi balaguro zuwa kasashe da suke fama da bala'in zazzabin Zika.

Cutar wacce sauro ke yadata tafi yawa a kasshe da suke Latin Amurka,musamman Brazil, kuma tafi zama musiba babba ga mata masu juna biyu.

Likitoci suna jin cutar tana aukawa kwakwalwa da hanyoyin aikewa da sakonni a jikin Dan'Adam, lamari da yake sa ake haifar yara da kananan kai da kuma kwakwalwa da rabinta baya aiki kamar yadda ya kamata.

Kasar Brazil ta bada rahoton cewa akwai mutane fiyeda dubu hudu wadanda suka kamu da wannan cuta tun cikin watan Oktoban bara. Amma kan kwararru ya daure kan dalilan da suka sa cutar kusan babu ita a wasu kasashen Latin Amurka yanki da cutar take da karfi.

Jiya Alhamis ne kasar Spain ko Andalusiya ta tabbatar cewa wata mace mai juna biyu ta kamu da cutar bayan da tayi balaguro zuwa kasar Columbia. Ita ce ta farko a turai da aka tabbatarta kamu da cutar.

Zuwa yanzu dai babu maganin cutar zika. Amma kamfanonin harhada magunguna a fadin duniya suna kokarin ganin sun hada maganin.

XS
SM
MD
LG