Ita wannan mata na kan fafutukar tsayar da wani akin hakar Dam din ka iya zama hatsari ga al’umma ne kafin a kasheta. Magoya bayan ‘yar gwagwarmayar sun dauko akwatin gawarta daga gidan mahaifiyarta zuwa Coci.
Inda suna tafe suna rera take da ke cewa, “Berta Na Raye”, sannan tare da yin kira ga yi mata adalci akan kisan gillar da aka mata. A shekarar 2015 da ta gabata, Caceres dai ta samu lambar yabo game da kare muhalli da ake kira Goldman Environmental Prize.
An dai kashe wannan ‘yar talika ne a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai mata har gida. Harin da ake zargin an shirya shi ne musamman don hallaka ta. To amma an cafke akalla mutum daya bisa zargin alaka da kisa.
Tuni dai dama gwamantin Honduras ta sa ana tsaron lafiyarta saboda yawan barazanar da ake mata, duk da yake dai ta sha kukan jami’an tsaron nata na sakaci sosai.