Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar ZIKA Na Iya Zama Barazana Ga Duniya Fiye Da Cutar Ebola


Daniele Ferreira
Daniele Ferreira

Wasu kwararrun a fannin lafiya suna hasashen cewa cutar nan ta ZIKA da ta bullo daga Kudancin Amurka na iya zama barazana ga lafiyar duniya fiye da cutar Ebola da ta kashe mutane fiye da 11,000 a kasashen Afirka.

Masanan lafiyar sun bayyanawa Jaridun Guardian da kuma wata mai suna Examiner a hirarraki daban-daban da suka yi da su gabanin taron hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da zai yanke hukuncin ko cutar na rukunin annobar cututtukan duniya da ke barazana ga bil’adama.

Hukumomin lafiyar kasar Brazil suna ta bayyana yadda ake samun karuwar yaran da ake Haifa da yan mitsi-mitsin kawuna wanda ya ninnaka yawan yadda aka dan saba samu jifa-jifa da kimanin rubi 10.

Har yanzu dai ana kan binciken gano musabbabin wannan muguwar cuta, to amma ana kyautata zaton alakantan yanayin yaduwar cutar tsakanin mata masu juna biyu ababen haihuwarsu.

XS
SM
MD
LG