Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaban Amurka Zai Jagoranci Taron Koli Da Kasashen Yankin Baltic


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Taron da kasashen yankin Balti zai zama wa Shugaban Amurka tamkar zakaran gwajin dafi a kungiyar taro ta NATO, saboda ya sha zargin kasashen da kasa adana kashi biyu na tattalin arzikinsu domin tsaro

Za'a haska fitila kan dangantakar Amurka da kawayenta a kungiyar tsaro ta NATO a wannan makon, lokacinda shugaban Amurka Donald Trump zai jagoranci taron koli da kasashen da suke yankin Baltic a fadar White House yau Talata.

Kamar yadda bayanai daga fadar white suke nunawa, shugaba Trump tareda shugaba Kersti Kaljulaid na Estonia, da shugaba Raimonds Vejonis,na Lativa, da shugaba Dalia Grybauskaita ta Lithuania sun kimtsa su gudanar da shawarwari don karfafa tsaro, cinikayya, da makamashi, da al'adu tsakanin Amurka da wadannan kasashe kawayenta a kungiyar tsaro ta NATO.

Haka nan fadar ta shugaban Amurka tace taron shugabannin zai nuna irin nasarori da kasashen suka samu wajen cika alkawarin bunkasa kudade da suke ware wa domin tsaro kamar yarjejeniyar da suka kulla a karkashin kungiyar ta NATO.

A farkon kama aikinsa, shugaba Trump, ya sha sukar kasashen dake cikin kungiyar tsaron ta NATO domin sun kasa ware kashi biyu cikin dari domin harkokin tsaro.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG