Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Kasuwar Hannayen Jari Ta Fadi A Nan Amurka


Kasuwar hannayen jari ta fadi jiya a nan Amurka
Kasuwar hannayen jari ta fadi jiya a nan Amurka

Sanadiyar martanin da China ta mayar wa Amurka yayinda ta dorawa wasu kayayyakin Amurka 120 karin haraji da kuma caccakar da Shugaba Trump ke yiwa kamfanin Amazon, hannayen jari sun fadi a kasuwa jiya

Kasuwar hannayen Jari ta Amurka ta sake faduwa ko a jiya Litinin,bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya fara sukar katafaren kantin zamani ta yanar gizo, wato Amazon,da kuma martanin China na azawa wasu kayayyaki daga Amurka karin kudin haraji, a rikicin cinikayya dake kara karfi.

Kasuwar tayi hasarar maki 589, ta fadi da kamar kashi biyu.A sashen kasuwar na manyan kamfanoni kamar masu hahadar motoci jari yayi kasa da kashi 2.3, yayinda bangaren fasaha da wasu kere-kere ya yi kasa da kusan kashi uku.

Shugaba Trump ya tasa Amazon a gaba sosai sau uku a cikin 'yan kwanakin da suka wuce. Kamar yadda watakil ba zaku kasa sani ba, mai kamfanin Amazon Jeff Bezos, shine mai mai kamfanin jaridar Washington Post, jaridar da take wallafa rahotanni kan shugaba Trump da gwamnatinsa, lamarin da bai yiwa shugaban na Amurka dadi ba.

Ahalinda ake ciki kuma,China ta kara kudin fito da kashi 25 kan wasu kayayyakin 120 dake shiga kasar daga Amurka, da suka hada da naman alade, kayan marmari,da wasu kayayyaki da kudin su ya kai dala milyan dubu uku.

Karin kudin harajin wadda ya fara aiki nan take daga jiya Litinin, a daren lahadi ne hukumomin China suka bada sanarwar daukar matakin, a zaman martani kan karin kudin fito da Amurka ta yi kan karafa da dalma wadda ya fara aiki daga ranar 23 ga watan Maris.

Ramuwar gayyar tana zuwa ne a dai dai lokacinda aka shiga zaman dar dar ta fuskar kasuwanci tsakanin hukumomin kasashen biyu.

Koda kuwa karin kudin harajin da China tayi ba zai yi wata illa ba ga tattalin arzikin Amurka mai karfin kudi zambar ko trillion 20, matakin zai yi tasiri ko jawo radadi ga wasu sassa na al'umar Amurka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG