Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Yi Watsi Da Shirin Kare Yaran Da Aka Shigo Dasu Kasar Tun Suna Kanana


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka ya yi watsi da shirin da ya kare yara kanana da aka shigo dasu ta barauniyar hanya dake da lakabin DACA saboda ba'a sakarwa jami'an shige da fice mara ba, Mexico kuma tana barin mutane na kwararowa cikin kasar


Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Lahadi, yayi kira da a kafa tsauraran dokokin shige da fice,kuma ya lashi takobi cewa zai dakatar da shirin ba matasan da aka shigo da su Amurka tun suna kanana izinin zama kasar, shirin da ake yiwa lakabin DACA a takaice.


Trump ya dora a shafinsa na Twitter a jiya da safe cewa ba a sakarwa jami’an tsaro dake sintiri a kan iyaka mara su gudanar da ayyukansu, saboda dokoki da masu sassaucin ra'ayi suka kafa "wanda ya ayyana a kama, daga bisani a saki bakin hauren."

Yace lamarin na kara zama mai hadari, yanzu ayari ayari ke shigowa Amurka saboda su amfana karkashin sabon shirin na DACA.


An bullo da shirin bada matsuguni ga yaran da aka shigo da su Amurka tun suna kanana ko kuma DACA ne loakcin gwamnatin shugaba Obama kuma shirin ya baiwa yaran da aka shigo dasu Amurka ta barauniyar hanya izinin zama da yin aiki a Amurka.


Gwamnatin Trump ta kawo karshen shirin a cikin watan Satumba, amma kuma ta ba majalisun kasar dama su fito da tsari na dindindin a kan makomar masu amfana da shirin.


Tun da farko Trump yace zai amince da ci gaban shirin DACA ne, indai majalisun kasar sun tabbatar da kudaden da za a aiwatar da gina katanga a kan iyakar kudancin kasar da Mexico.

A wani sakon Twitter da ya aike da safiyar jiya Lahadi, Trump ya dora laifi a kan Mexico cewar bata yin wani abu domin hana bakin haure kwarara zuwa Amurka, kuma yana barazanan dakatar da yarjejeniyar cinikayya da Mexico, saboda hakan.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG