Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Zanga-Zanga A Califonia Sakamon Kashe Wani Bakar Fata


An gudanar da zanga-zangar domin nuna kyamar yadda 'yan sanda suka kashe wani dan taliki a Califonia bada hakkin sa ba.

Tsohon dan wasan kwallon kwandon nan ne a jiya asabar ya jagoranci zanga-zagar a Sacremento dake jihar Califonia na nan Amurka, inda yake kira da rundunar ‘yan sanda da su bada cikakken bayanin yadda aka kashe Stephen Clark wani bakar fata a ranar 18 ga watan maris.

Gangamin na jiya ya biyo bayan irinsa wanda akayi ne a ranar jumaa inda daruruwan masu zanga-zanga bayan an gudanar da bincike mai zaman kansa da ya gano cewa an harbi wannan dan taliki ne wato Clark da harsasai har bakwai a lokaci guda, wanda hakan yayi karo da bayanan da ‘yan sanda suka bayar da farko.

Sai dai jamian tsaro sunyi dafifi a wajen wannan zanga-zangar.

Mutane masu tarin yawa suka halarci wannan gangamin ciki ko harda budurwan Clark da zai aura, tabi sahun masu zanga-zanga a wurin taron jamaa dake Sacramento.

Hakama ranar asabar din da ake gudanar da wannan zanga-zangar yazo dai-da da ranar tunawa da Ceser Chavez, domin jihohi anan Amurka ciki ko harda Califonia na cikin wadanda suka tuna wannan mutumin dan kasar Spaniya wanda ya sanmar da kungiyar manoma.

Masu zanga-zangar na ranar asabar suka ce zasu karrama Chavez shida Clark a lokaci wannan zanga-zangar tasu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG