Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maiyuwa Trump Ya Janye Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump da Theresa May ta Ingila.
Shugaban Amurka Donald Trump da Theresa May ta Ingila.

Batun yarjejeniyar Nukiliyar Iran ta taso ne a tattaunawar da shugaban Amurkan yayi tareda Frayin Ministan Ingila Teresa May ta woyar tarho a ranar Asabar, mako daya kamin Amurka ta ci gaba da mutnuta shirin ko ta janye.

Shugaban Amurka Donald Trump yayi magana da PM Ingila Theresa May, jiya Asabar kan batutuwa da suka hada da yarjejeniyar Nukiliyar Iran,mako daya kamin shugaban na Amurka ya yanke shawara ko Washington zata fice daga cikin yarjejeniyar, kamar yadda fadar white House ta shugaban na Amurka ta fada.

Mr. Trump yana da zabi daga nan zuwa 12 ga watan nan na Mayu, ya janye daga yarjejeniyar da Tehran ta kulla da manyan kasashen duniya ciki harda Amurka a shekara ta 2015. Jami'an Fadar white House suka ce shugaban kusan ya yanke shawara zai janye kamar yadda suka fada ranar 2 ga watan nan.

Duk da haka shugaban na Amurka yana iya bullo da wata hanya na ci gaba da mutunta yarjejeniyar da jamhuriyar Iran mai bin tafarkin islama ta kulla da sauran manyan kasashern duniyar ciki harda Amurka.

Britaniya, da Jamus, da Faransa duk sun yi itifakin cewa yarjejeniyar itace hanya daya da zata hana Farisa mallakar makaman Nukiliya.

A hirar da suka yi tawayar tarho da PM May, Mr.Trump, ya jaddada kudurinsa na ganin cewa Iran bata mallaki makaman Nukiliya ba har abada, inji fadar ta White House.

Haka nan shugabannin biyu sun yi magana kan batun Nukiliyar koriya Ta Arewa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG