Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iran Ya Gargadi Amurka Kan Watsi Da Yarjajjeniyar Nukiliya


Shugaba Hassan Rouhani
Shugaba Hassan Rouhani

A cigaba da takaddamar da ake yi kan yarjajjeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, Iran ta ce muddun Amurka ta yi watsi da yarjajjeniyar, ita ma za ta wancakalar da ita.

Shugaban Iran, a yau dinnan Lahadi, ya ce muddun Amurka ta janye daga yarjejjeniyar nukiliyar da aka cimma tsakaninta da manyan kasashen duniya, labudda Amurka za ta yi dana-sani.

Hassan Rouhani ya fada a wani jawabinsa da aka yada ta gidan talabijin cewa, “Idan Amurka ta janye daga yarjajjeniyar ta nukiliya, ba da jimawa ba za ku ga cewa ta yi wani irin da na sanin da ba ta taba yi ba a tarihi.”

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yanke shawara zuwa ran 12 ga watan Mayu kan ko Amurka za ta cigaba da mutunta yarjajjeniyar ta nukiliya ko a’a.

Trump dai ya ce zai fice daga yarjajjeniyar idan ba a yi wasu gyare-gyare ba, ciki har da wani tanaji na takaita shirin makami mai linzami na Iran, wanda Iran ta ce saboda kariya da kuma tauna tsakuwa ta ke yinsa.

Hasali ma Ministan Harkokin Wajen Iran, ranar Alhamis ya ce Iran ba za ta yadda da yin wani kwaskwarima ga yarjajjeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG