Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaba Obama Zai Kammala Ziyarar da Yake Yi a Afirka


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama na kammala ziyar da ya kai kasashen Kenya da Ethiopia a nahiyar Afirka.

Yau Talata ne shugaba Obama zai kammala ziyarar sa da yakai a kasashen Africa ta Gabas. Obama shi shugaban Amurka na fark na dake kan karagar mulki yayi wa taron kungiyar tarayyar Africa jawabi a babban ofishin kungiyar dake babban birnin kasar Habasha.

Jawabin sa ga kungiyar a Adisa Ababa ya biyo bayan ganawar sa ne da magatakardan kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma, wanda kuma daga bisani suka kai ziyara a kanfanin sarrafa abinci.

A jiya ne dai shugaba Obama yayi tattaunawar kiki da kiki da Prime Ministan Ethiopian Hailemariam Desalengn, cikin batutuwan ko da suka tattaunan sun hada da maganar barin yan jarida da yan adawa suna bayyana ra'ayin su bada tsangwama ba.

Yace barin wadannan su fadi albarkacin bakin su zai kara wa jamiyya mai mulki tagomashi musammam wajen tafiyar da harkokin ta.

Mr Hailemarian yace kasar Habasha tana iya bakin kokarin ta na inganta harkokin hakkin bil adama. Yace kokarinsu na mutunta demokaradiyya na zahiri ne ba na jeka nayi ka ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG