Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya bar Kenya zuwa Ethiopia


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

A yau lahadin shugaban Amurka Barack Obama ya kammala ziyararsa a kasar Kenya tushensa, bayan yin jawabi mai ratsa jiki akan ziyarar tasa.

Daga nan kuma zai sauka a Adis Ababa a matsayin shugaban Amurka na farko da ya ziyarci kasar Ethopia. Ya kamala ziyarar ne da halartar liyafar da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya shiya masa.

Obama yayi nuni da cewa mahaifinsa da mahaifin Uhuru na Kenya sun san juna, yace bai san farin cikin da zasu yi ba inda zasu san ga ‘ya’yansu a waje daya.

Mista Obama ya jaddada cewa Amurka da Kenya zasu hada karfi da karfe wajen yakar ta’addancin ‘yan kungiyar Al-Shabaab na Somalia.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG