Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama yace zaben Burundi bai inganta ba


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

Shugaban Amurka Barack Obama yace zaben da aka yi a Burundi bai ninganta ba sannan yana kira da a tattauna tsakanin gwamnati da ‘yan adawa.

Yace sun tattauna game da zaben Burundi shi da shugaban Kenya, inda suke son a tattauna a siyasance don gudun yakin da zai hallaka wadanda basu ji basu gani ba.

Sai dai Ministan harkokin wajen Burundi Alan Nyamitwe yayi watsi da wannan batu a Adis Ababa da cewa ba wanda ya isa ya canza abinda ‘yan Burundi suke so.

‘Yan jam’iyyun adawa a kasar sun yi tir da wannan sakamakon zabe tare da kiran a sake yin wani zaben bisa sahihanci.

Gaba daya ma dai kauracewa zaben suka yi da cewa Pierre Nkurunziza ya saba ka’idar kundin tsarin mulki ta wa’adin yin mulki sau biyu kacal.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG