NIAMEY, NIGER - Kungiyar agaji ta kasa da kasa ICRC wacce ke kula da taimaka wa mutanen da irin wannan al’amari na bacewar dangi ya same su kan yi amfani da zagayowar wannan rana don fadakar da al’umma akan hanyoyin bada cigiya a ofisoshinta.
Madame Sarra Magri Shugabar sashen kula da ba da kariya a kungiyar agaji ta kasa kasa CICR ko ICRC reshen Nijar ta yi wa manema labarai bayani dangane da makasudun ranar mutanen da suka bace.
Ta ce magana ce ta ayyukan jin kai kasancewar abu ne da ke shafar al’ummomi da dama. Duba al’amar masu rigingimau na kan gaba wajen tarwatsa iyalai da haddasa bacewar mutane.
Ba’idin yake matsalar zuwa ci rani na daga cikin manyan dalilan da ke sanadiyar bacewar mutane a Afrika musamman a wannan yanki inda ketara kogin Mediteraneen kan zama sanadin bacewar wasu da dama.
Wannan yasa kungiyar CICR ke kokarin ankarar da duniya mahimmancin bai wa fannin kulawa sosai don ganin an taimaki mutanen da suka bace da iyalan wadanda irin wannan matsala ta same su.
Domin tunkarar wannan babban kalubale kungiyar CICR ta shimfida wani tsarin bin diddigi a yunkurin neman mutanen da danginsu suka bada cigiya.
Wasu mazaunan yankin Tilabery da suka bada cigiyar danginsu a ofishin CICR sun yi mana karin haske kan faruwar wannan al’amari da hanyoyin da aka bi.
Lura da yadda mutane da dama ba su san tudun dafawa ba bayan bacewar wani nasu ya sa kungiyar agaji kara karfafa hanyoyin fadakarwa domin gwada wa al’umma hanyoyin bi.
Dalilai masu nasaba da yanayin zamantakewar al’umma kokuma abubuwan da suka shafi rayuwar iyali wani bangare ne na tarin matsalolin da ke mafarin bacewar mutane.
Haka kuma kawo yanzu babu wasu alkalumma a hukunce game da adadin mutanen da suka bace a nan cikin gida Nijar har zuwa kasashen nahiyar Afrika.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna