Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirkiro Sabuwar Jiha a Najeriya


Majalisar Tarayya, a birnin Abuja dake Najeriya.
Majalisar Tarayya, a birnin Abuja dake Najeriya.

Masu neman a kirkiro sabuwar jiha a kudu maso gabashin Najeriya sun bada dalilai na aiwatar da hakan.

An yi kira da a kirkiro wata sabuwar jihar a kudu maso gabashin Najeriya, a ci gaba da taron kasa da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Tarayya Abuja.

Wakiliyar Muryar Amurka a zauren taron Medina Dauda, tace masu taron na kasa sun raba kawunansu cikin kwamitoci ashirin da daya, kuma suna tarurukansu a wurare biyu ne.

Masu neman a kirkiro sabuwar jihar sun bada dalilan cewa cikin shiyyoyi shida da ake dashi a Najeriya, kowace shiyya nada jihohi shida-shida ne sai kudu maso gabashin ne kawai ke da jihohi biyar.

Daya daga cikin kwamitocin kuwa, sun yi magana ne game da arzikin kasa da ake da shi inda suka kwatanta aikin noma dake arewa, da kuma man fetur dake jihohin Neja Delta.

An yi misali cewa bai kamata a kwatanta aikin noma da mai da ake dashi a jihohin Neja Delta ba, saboda kuwa ka ga mai abun ne da Allah ya wadata shi an san da zaman sa awuri guda shikuwa noma harka ne da mutane ke yi.

Kuma wakiliyar ta kara da cewa "yan kwamitin suka ce kudaden gwamnatin tarayya da ake ba jihohin arewa bai taka kara ya karya ba, wato ma’ana bai isa sun wadata alumarsu da kayan more rayuwa na damokradiya kamar yanda ake samu a wadanna jihohi dasuke da arzikin albarkatun main fetur ba."

Maganar baiwa shugaban kasa wa’adin shekaru shida wanda majalisar kasa tayi watsi dashe ya kuno kai a taron kasa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG