A yayin da tsagaita wutar ta fara aiki, anga jerin motoci sun nufi kudancin Lebanon, inda aka shafe watanni ana gwabza kazamin fada da kuma umarnin Isra'ila na tilastawa mutane barin gidajensu.
Sojojin Isra'ila sun gargadi mutane da su kaurace wa kauyukan da a baya suka ba da umarnin ficewa.
Amurka tare da Faransa sun taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin, wanda majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta amince da shi da yammacin jiya Talata.
Shugaban Amurka Joe Biden ya kira tsagaita wutan “Mataki mai mahimmanci… don kawo karshen tashin hankali” a Gabas ta Tsakiya. Ya ce Iran da 'yan ta'addanta, Hezbollah a Lebanon da kuma mayakan Hamas a Gaza, “sun yabawa aya zakinta” a cikin sama da shekara guda suna fafatawa da sojojin Isra'ila.
Ya ce yarjejeniyar Isra'ila da Hizbullah “an tsara ta ne domin ta zama ta dindindin ta dakatar da yaki.”
Dandalin Mu Tattauna