Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ya Kara Kudin Ruwa Zuwa Kaso 27.5 Cikin 100

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso (Hoto: Facebook/CBN)
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso (Hoto: Facebook/CBN)

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Yemi Cardoso ne ya sanar da hakan a Abuja a yau Talata yayin taron kwamitin manufofin kudin bankin na karshe a bana da ya gudana a shelkwatar babban bankin.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara yawan kudin ruwa a kan basussuka (MPR)daga kaso 27. 25 zuwa kaso 27.50 cikin 100 a wani yunkuri na yaki da hauhawar farashin kayan masarufi.

Hakan ya biyo bayan taron kwamitin manufofin kudi (MPC) na babban bankin Najeriyar.

Da ma’aunin MPR ake auna araha ko tsadar bashi.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Yemi Cardoso ne ya sanar da hakan a Abuja a yau Talata yayin taron kwamitin manufofin kudin bankin na karshe a bana da ya gudana a shelkwatar babban bankin.

Cardoso yace gaba-dayan mambobin kwamitin na MPC ne suka amince da kara kudin ruwa da maki 25 daga kaso 27.25 zuwa kaso 27.50 cikin 100, tare da barin adadin tsabar kudi a kan kaso 50 cikin 100 ga bankunan ajiya da kaso 16 cikin 100 ga bankunan hannayen jari.

Wannan shine karo na 6 da CBN ke kara yawan kudin ruwan tun cikin watan Fabrairun 2024.

A watan Satumba, bankin ya kara kudin ruwan zuwa kaso 27.25 cikin 100 sakamakon raguwar da hauhawar farashin kayayyaki ta yi a watan Agustan 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG