Daruruwan gidaje a Ingila da Wales sun yi taho-mu-gama da ambaliyar ruwa a ranar Litinin, kuma ma’aikatan jirgin kasa da dama sun soke aiyukansu bayan da guguwar Bert ta afkawa Birtaniyya da ruwan sama mai karfin gaske da iska mai karfin mitoci 80 a karshen mako.
Ruwan sama ya kai milimita 130 a wasu yankunan, lamarin da ya sa wasu kogunan suka cika suka tunbatsa tare da mayar da hanyoyi zuwa magudanar ruwa.
Wani mutum mai shekaru 80 da haihuwa ya mutu bayan motarsa ta shiga ruwa a wani makeken ruwa da ke Lancashire a arewa maso yammacin Ingila a ranar Asabar, kuma an tsinci gawar wani mai kula da kare da ya bace a wannan rana, a kusa da kogin Afon Conwy da ke Arewacin Wales.
Sakataren muhalli Steve Reed, ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa, “Abin bakin ciki ne za a kara samun ambaliyar ruwa a cikin 'yan kwanaki masu zuwa yayin da matakan ruwa ke karuwa a kogunan da ke gudana a hankali kamar Severn da Ouse.”
Haka kuma ya kara da cewa “Hukumar Muhalli tana tsammanin cewa tasirinta zai ragu ba kamar yadda aka gani a cikin 'yan kwanakin nan.”
Fiye da sanarwar ambaliyar ruwa 130 sun kasance suna aiki a cikin Ingila da Wales da kuma Scotland da yammacin Litinin.
Dandalin Mu Tattauna