Majalissar dokokin Najeriya ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar suka hada kai da masu fafutuka, domin gudanar da wani gangamin da aka fi sani da “kwana 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata”.
Daruruwan mutane ne da suka hada da masu fafutukar kare hakkin mata, da ‘yan majalisar dokokin Najeriya, da sauran mahalarta taron, suka yi ta rera waka yayin da suke tattaki daga majalisar dokokin kasar a kan titunan Abuja ranar Litinin.
Muzaharar dai wani bangare ne na shigar Najeriya cikin yakin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke yi na yaki da cin zarafin mata, ko kuma GBV, wanda zai gudana daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba.
Sai dai kuma wata dama ce ta sanar da sabon yunkurin da hukumomi ke yi na magance cin zarafin mata a Najeriya.
Abbas Tajudeen kakakin majalisar wakilan Najeriya ne ya jagoranci ‘yan majalisar zuwa taron. An gudanar da bikin cika shekaru 25 na ranar kawar da cin zarafin mata ta duniya.
Ya ce “Kowane minti 10 ana kashe mace a fadin duniya, wannan lamari ne da ba za a amince da shi ba, wannan lamari ne da ba za a yafe ba, mu a majalisa dole ne mu hada kai fiye da kowane lokaci da hukumomin da abin ya shafa, musamman jami’an tsaro wajen ganin mun tabbatar da cewa mun yi hakan, don dakatar da wannan al'ada mai hadari.”
Cin zarafin jinsi matsala ce ta duniya. Hukumomin Najeriya sun ce kusan kashi daya bisa uku na mata masu shekaru 15 zuwa 49 na fuskantar cin zarafi ta jiki da na lalata a rayuwarsu.
Har ila yau kasar tana da kusan mutane miliyan 20 da suka tsira daga GBV - ko kuma kusan kashi 10 cikin 100 na jimlar duniya.
Rashin wayar da kan jama'a da karancin rahotanni da son kai a al'adu da addini, da kuma rashin amana a cikin tsarin shari'a na daga cikin kalubalen da ke kawo cikas ga kokarin magance cin zarafin jinsi a Najeriya.
Yayin da hukumomi ke ci gaba da kokarin shawo kan matsalar, mutane da yawa na fatan sabon tsarin zai samar da hanyar rayuwa ga miliyoyin mutane masu rauni.
Afirka ta sami mafi girman adadin cin zarafi daga abokan hulda da mace mai alaka da dangi a bara, sai Amurka da Oceania, a cewar Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Laifuka da miyagun kwayoyi.
Dandalin Mu Tattauna