An kai harin ne lokacin da masallata ke idar da sallar isha'i. Masallatan sun hada da Alhaji Musa Sale hakimin Kwankwaso kuma majidadin Kano. Lamarin ya jefa mutanen garin cikin dimuwa da firgicewa musamman wadanda ke cikin masallacin har da yara kanana.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku nan take wasu goma kuma sun samu muggan raunuka. Wasu kuma da suka hada da Alhaji Musa Sale Kwankwaso Allah ya yi masu gyadar dogo.
An garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibitin koyaswa na Malam Aminu Kano cikinsu har da wani karamin yaro dan shekaru shida da yake kukan a bashi ruwa ya sha.
Wani Anas Umar Kwankwaso wanda ya tsira da ransa daga harin ya ce sun gama salla ana yin sallama sai suka ji harbi ko ta ina. To da yake wasu cikin masallacin jami'an tsaro ne kuma suna da bindigogi sai suka soma mayarda martani. Bayan kura ta lafa aka san maharan sun kashe mutum uku kuma sun raunata wasu da dama. Shi ma Anas ya dan samu rauni.
Kawo yanzu babu wani bayani daga hukumar 'yansandan jihar Kano ko kuma gwamnatin jihar.
Ga karin bayani.