Wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta nemi bayanai wurin 'yansanda da mutanen da abun ya shafa da jami'an gwamnatin jihar Filato. Mataimakin jami'in yansanda dake hulda da jama'a ASP Dominic Etim ya shaida mata cewa wasu 'yanbindiga ne da ba'a san ko su wanene ba suka bude wa mutane wuta a kauyen Maikatako dake cikin karamar hukumar Bokkos.Lamarin ya faru ne daren Talata daidai lokacin da mutane kauyen ke bikin tarbar sabuwar shekara a dandalin wasan kauyen bayan sun fito daga mijami'a.
'Yan bindigar sun harbe mutane biyu har lahira nan take inji jami'in 'yansandan. Mutane goma sha hudu suka samu raunuka wadanda aka garzaya da su asibiti a cikin garin Barikin Ladi.
Karin bayani daga mutanen kauyen ya ce kawo yanzu mutane uku ne suka mutu wasu kuma su hudu suna asibitin koyaswa na jami'ar Jos rai hannun Allah.
Kawo lokacin wannan karin bayani jami'an tsaro basu cafke kowa ba daga cikin maharan sabo da abun ya faru ne da daddare kuma bayan sun yi harbin suka ruga da gudu.
Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da a ke zaton an samu lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Filato. Jama'ar yankin suna nuna matukar mamaki kamar yadda kwamishanan gidaje da raya birane wanda ya fito daga yankin ya bayyana. Ya ce jama'a suna ta mamaki domin basu yi fada da kowa ba ko wani tashin hankali. Sun nuna mamaki ganin cewa an samu zaman lafiya a duk fadin jihar.
Kawo yanzu dai kantomar karamar hukumar Hannatu Dantong ta ce suna kan taro da jam'an tsaro. Ta ce idan sun gama taronsu zata bayyani matakin da gwamnati ta dauka.
Ga rahoton Zainab Babaji.