Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Sun Kashe Wani Malamin Addinn Musulunci a Buratai


'Yansanda suna sitir bayan an kai hari
'Yansanda suna sitir bayan an kai hari

Wasu 'yanbindiga da ba'a tantance ba su kimanin goma sha takwas sun kashe wani malami a cikin gidinsa a garin Buratai.

A garin Burutai dake jihar Borno wasu 'yanbindiga sun kai hari gidan wani malamin addinin Musulunci suka kasheshi har lahira nan take.

Malam Buba wani mazaunin garin Buratai da ya ga lamarin ya yi bayani. Lamarin ya faru ne ranar Lahadi. Malamin wanda aka sani da suna Malam Abba yana zaune cikin gidansa suka yi sallama. Su 'yanbindigar sun zo ne cikin motoci kirar hilux sanye da rawuna a kawunansu dukansu kuma dauke da bindigogi. 'Yanbindigan sun fi goma sha takwas. Da shigarsu suka harbe malamin. Basu taba kowa ba saidai wani saurayi da suka kama. Har sun fara tafiya da saurayin sai suka tambayeshi takardar shaida wadda ya ce bashi da. Daga bisani suka sakeshi.

'Yanbindigan basu taba kowa ba banda shi Malam Abba. Bayan sun tafi kuma babu wasu jami'an tsaro da suka biyo baya su yi bincike.Lamarin ya faru waje-jen karfe bakwai na safe ne. 'Yanbindigan sun bincike gidan malamin. Sun ga wasu buhunhuna wadanda suke tsammanin kudi ne cikinsu. To sai dai ba kudi ba ne. Sun tafi da babur da malamin ke hawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG