Wannan sanarwar ta 'yansandan ta biyo bayan an kashe wasu 'yan siyasa guda biyu ne da ya faru a garin Gombe daren Talata. DSP Attajiri kakakin 'yansandan ya ce daren Talata wasu batagari suka je wata anguwa suka hau katangar gidan Adamu Yusuf da aka sani da suna Kula da kuma gidan Alhaji Umar Makama. Adamu Yusuf da Umar Makama sun rasu. Na ukun da suka harba Abubakar Yayado yana asibiti. Ya kira mutane su taimakesu da labarin da zai kai ga kama mutanen da suka yi aika-aikar. Ya ce za'a bada tukuici ga duk wanda ya bada labarin da ya taimaka.
A wani gefen kuma masu 'yan radun kare hakin dan adam sun fara bayyana matakan da zasu dauka a kan irin wannan aikin ta'adancin. Shugaban kungiyar adalci ta jihar Gombe ya ce kashe-kashe da 'yan kalare ke yi ya yi yawa. Ko jiya wurin raba kudin da aka basu game da aikin kashe-kshe ya haddasa rikici tsakaninsu har ya kai ga kisan kai. Ya ce a matsayinsu na kungiyar adalci ba zasu yadda da kashe-kashe ba. Ba zasu yadda a cigaba da yiwa rayuwarsu barazana ba, Ya ce zasu tuntubi wasu kungiyoyin kare hakin bil adama da wasu ma su san abun da zasu yi domin a dakatar da kisan mutane. Ya ce ba zasu yadda daukan rayukan mutane domin cimma muradun wasu 'yan siyasa.
Ibrahim Garba Iwala dan radun kare hakin dan adam a arewacin Najeriya ya ce abun da ya faru suna tuhumar gwamnatin jihar tukunna domin akwai jita-jita cewa an baiwa wasu yara kudi nera miliyan goma sha shida su raba. To a kan menene aka basu? Ladan aiki ne da suka yi? Ko kyauta ce kawai aka basu? Tuhuma ta biyu ta 'yansanda ce. Tunda kwamishanan 'yansandan ya ce ya sa jami'ansa a kowane lungu yaya aka yi wannan abun ya faru? Tabbas su bada amsa da zata gamshesu ko kuwa su san matakan da zasu dauka.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.