Dokar da ta hana sana'ar achaba da yin kabu-kabu da hana hawan babura da goyo a duk fadin babban birnin jihar, Minna, zata fara aiki yau. Tuni dai talakawan garin suka fara kokawa tare da yin fargaba ganin dimbin masu sana'ar zasu rasa aikin yi lamarin da ka kai ga yawan barayi da 'yan fashi. Kungiyar 'yan kabukabu ta ce kimanin 'yan kungiyar wajen dubu uku zasu rasa aikin yi daga yau inji shugaban kungiyar Musa Isiyakau. Ya ce suna da 'yan kungiyar kusan dubu hudu to amma kekunan keke napep dubu daya gwamnati ta tanada. Suna bukatar a kara masu dubu uku domin dakile zaman kashe wando.
Kungiyoyin kare hakin talakawa sun sha yin kiraye-kiraye tare da janyo hankalin gwamnatin jihar Neja ta janye dokar. Kungiyar Muryar Talaka na cikin wadannan kungiyoyin. Alhaji Murtala Maigyada shugaban kungiyar a jihar Neja ya ce gaskiya dokar zata cutar da talakawa musamman wadanda suke yin sana'ar a gefe daya kenan. Ta wani gefen kuma talakawa ne suka fi anfani da achaba zuwa gidajensu da wuraren sana'o'insu da zuwa wasu wurin biyan bukatunsu. Su ne dokar zata takurawa. Ya ce kungiyar muryar talaka tana kiran 'yan majalisar dokokin jihar su jawo hankalin gwamnan jihar domin ya kawar da dokar.
Umar Bago mai wakiltar birnin Minna a majalisar wakilan kasar Najeriya ya kira wani taron manema labarai a kan wannan lamarin. Ya ce idan an dakatar da sana'ar achaba do a yi kokari a samarda isassun wasu ababen hawa domin taimakawa jama'a. Kwamishanan sufuri na jihar Alhaji Garba Mohammed wanda ya ce dokar zata fara aiki yau kuma duk wanda aka kama za'a hukuntashi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari