Kwana daya kafin aukuwar lamarin, kungiyar HTS da kungiyoyin da ke kawance da ita, sun kai wani harin ba-zata a yankunan da ke karkashin ikon gwamnati a arewacin lardin Aleppo, lamarin da ya haddasa kazamin fada da ba a ga irinsa ba cikin shekaru da yawa, a cewar kungiyar kare hakkokin bil'adama ta Observatory da ke Siriya.
Amurka da Turkiyya sun ayyana kungiyar HTS a matsayin kungiyar ta'addanci.
"Adadin wadanda aka kashe a fadan da ake ci gaba da gwabzawa ya karu zuwa 182, ciki har da mayakan kungiyar ta HTS 102, da wasu 19 daga kungiyoyin kawancen HTS, sai kuma sojojin gwamnati da mayakan kungiyoyin kawancensu 61," a cewar kungiyar sa idon.
Rasha dai abokiyar kawancen shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ce, a shekarar 2015 ta fara shiga yakin basasar na kasar Siriya.
Kungiyar ta HTS da kawayenta da suka hada da kungiyoyin da Turkiyya ke marawa baya, sun katse babbar hanyar M5 International ta Damascus zuwa Aleppo, bayan da suka mamaye mahadar manyan hanyoyin M4 da M5, a cewar kungiyar ta Observatory mai shelkwata a Birtaniyya.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce "fiye da mutane 14,000, da kusan rabinsu yara ne, sun rasa matsugunnansu" sakamakon tashin hankalin.
Sama da shekaru 10 kenan ana yakin basasa a kasar Siriya, ko da yake an samu raguwar rikicin a 'yan shekarun nan.
Dandalin Mu Tattauna