Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN AMURKA: Babu Zabi Mai Kyau Ga 'Yan Gudun Hijirar Siriya A Lebanon


U.N. - Ambasada Robert Wood
U.N. - Ambasada Robert Wood

A yayin da wutar rikicin gabas ta tsakiya ke matsawa zuwa Lebanon daga Zirin Gaza, fararen hula na arcewa zuwa kasashen makwabta.  tun daga ranar 23 ga watan Satumbar da ya gabata, fiye da mutane dubu 425 sun ketara zuwa Syria daga Lebanon, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Kimanin kaso 72 cikin 100 na mutanen 'yan Syria ne, wadanda yaki ya raba da muhallansu sau 2, kuma suka fuskanci mummunan hatsari a kokarin komawa kasarsu ta asali. Galibinsu sun gujewa yakin basasar kasarsu shekaru da dama da suka gabata kuma sun yi ta kokarin kaucewa yunkurin gwamnatin Syria na mayar dasu gida da karfin tuwo.

"Amurka ta yi matukar damuwa da halin da 'yan gudun hijirar Syria ke ciki a Lebanon da kuma farar hulal da rikici ya daidaita a Lebanon, a cewar Robert Wood, wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya kan al'amuran siyasa na musamman. "Suna fuskantar zabi mai wahalar gaske na kara arcewa a cikin Lebanon ko kuma su tsallaka kan iyakar Lebanon zuwa halin rashin tsaro a Syria.

“Muna kokarin taimakawa 'yan gudun hijira marasa galihu, da wadanda aka raba da muhallænsu da al'ummomin dake karbar baki a yunkurinsu na yin martani ga rikicin. A ranar 26 ga watan Satumbar da ya gabata, Amurka ta yi shelar bada gudunmowar kusan dala miliyan 534 a matsayin karin tallafin agaji ga al'ummar Syria, ciki har da tallafin kungiyoyin kasa da kasa suka bayar."

Amurka ta jinjinawa shawarar gwamnatin Syria ta kyale ofishin jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kan 'yan gudun hijira damar ganawa da masu komawa, kan iyaka dama yankunan da zasu koma, a cewar jakada Wood.

"Mun kuma yaba da shawarar gwamnatin Syria ta dakatar da cazar kudade daga 'yan Syria dake komawa kasarsu," a cewarsa. "Zamu cigaba da tallafawa kokarin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na inganta bada kariya ga muhalli a Syria."

“A wannan gaba, muna matukar damuwa da rahotanin ci gaba da cin zarafin masu komawa, ciki har da yadda gwamnati ke tsare masu komawar ba tare da wani dalili ba.”babu yadda za'a yi komawa ta zama bisa raddin kai da gaske kuma cikin aminci da mutunci sannan mai dorewa har sai gwamnatin Syria ta sauya halayenta tare da dabbaka 'yancin dan adam da kiyaye 'yancin kowa."

"Wajibi ne gwamnati da dukkanin bangarori a Syria su kyale kayan agaji su kai dukkanin sassan Syria nan take ba tare da wata cikas ba matukar aka ci gaba da samun bukatar hakan," a cewar jakada Wood.

"Amurka za ta ci gaba mutunta alkawuran da ta daukarwa al'ummar Syria da ma mutanen da aka raba da muhallansu a Lebanon kuma muna kira ga sauran masu bada agaji dasu hada hannu tare damu wajen cike gibin muhimmiyar bukatar kudade ta yadda hukumomin bada agaji zasu ci gaba da biyan bukatun marasa galihu."

Wannan sharhi ne na ra’ayoyin gwamnatin Amurka

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG