Rundunar sojin Isra’ila, wacce ta kai dimbin hare-hare a Syria tun bayan barkewar yakin basasar kasar a 2011, ta ki cewa komai game da hare-haren da aka ba da rahoton kaiwa a baya-bayan nan.
Da yake kafa hujja da wata majiyar likitoci, kamfanin dillancin labarai na kasar Syria (SANA) yace; “adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila a wurare da dama na yankin Masyaf ya karu zuwa mutane 14 tare da raunata wasu 43 ciki har da wadanda ke cikin mawuyacin hali mutum 6.”
Hukumar dake sanya idanu a kan kare hakkin bil adama lokacin yaki ta kasar Syria ta ba da rahoton cewa zafafa kai hare-haren da Isra’ila ta yi a cikin dare ya hallaka mutane 18 ciki har da mayakan Syria 8. Inda ta kara da cewa an raunata wasu 32.”
Galibin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Syria tun cikin 2011 sun fi maida hankali ne a kan sansanonin soji da mayakan kasar Iran ke marawa baya ciki har da kungiyar Hezbullahi ta kasar Lebanon.
Dandalin Mu Tattauna