Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Tawayen M23 Sun Tsagaita Wuta A Jamhuriyar Dimokiradiyyar Congo


Sanarwar da gamayyar kungiyoyin siyasa da na soja da ake kira da “kawancen kogin Congo” wanda M23 ke zama mamba ta fitar da maraicen jiya Litinin, tace za’a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta yau Talata a “bisa dalilai na jin kai.”

Kungiyar M23 mai gwagwarmaya da makamai dake samun goyon bayan kasar Rwanda ta ayyana tsagaita wutar bada agaji a bangarenta kawai tun daga yau Talata a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyyar Congo mai yawan fama da rikici, sakamakon kiraye-kirayen da ake ta yi na samar da hanyar da kayan agaji za su isa ga dubun dubatar mutanen da aka raba da muhallansu.

M23 ta bayyana cewa tsagaita wutar za ta fara aiki ne tun daga yau Talata.

Sanarwar ta jiya Litinin na zuwa ne jim kadan tun bayan da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar akalla mutane 900 ne aka kashe a fadan daya barke a makon daya gabata a birnin Goma dake gabashin jamhuriyar dimokiradiyar Congo tsakanin ‘yan tawayen da sojojin kasar.

Fada ya lafa a birnin mai al’umma fiye da miliyan 1, wanda mayakan M23 ke ikirarin karbe iko da shi tun a makon daya gabata, saidai rikicin ya fantsama zuwa gundumar kudancin Kivu dake makwabtaka, inda ya kara fargaba da ake da ita na cewar M23 na iya matsawa zuwa babban birninta Bukavu.

Sanarwar da gamayyar kungiyoyin siyasa da na soja da ake kira da “kawancen kogin Congo” wanda M23 ke zama mamba ta fitar da maraicen jiya Litinin, tace za’a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta yau Talata a “bisa dalilai na jin kai.”

Sanarwar ta kara da cewa “ba ta niyar karbe iko da birnin Bukavu ko wasu yankuna,” duk da cewa a makon da ya gabata M23 ta bayyana cewa tana son ta ci gaba da nausawa zuwa Kinshasa, babban birnin Congo.

A cikin fiye da shekaru 3 da aka shafe ana yaki, an ayyana yarjejeniyar tsagaita wuta da sulhu har sau 6, kafin daga bisani a rusa su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG