Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Congo Ta Yanke Huldar Diflomasiyya Da Rwanda


Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Felix Tshisekedi (Photo by FABRICE COFFRINI / AFP)
Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Felix Tshisekedi (Photo by FABRICE COFFRINI / AFP)

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke huldar diflomasiyya da Rwanda yayin da ake gwabza fada tsakanin ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda da dakarun gwamnatin a kusa da muhimmin birnin Goma na gabashin kasar.

Akalla dakarun wanzar da zaman lafiya 13 da sojojin kasashen waje ne aka kashe a yakin da ya kuma raba dubban fararen hula da gidajensu.

Kungiyar ‘yan tawayen M23 ta samu gagarumar galaba a kan iyakar kasar da Rwanda a cikin ‘yan makonnin da suka gabata tare da rufe garin Goma, babban birnin lardin mai kusan mutane miliyan biyu.

Congo, Amurka da kuma kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun zargi Rwanda da mara wa kungiyar M23 baya, wadda galibi ‘yan kabilar Tutsi ne da suka balle daga sojojin Congo fiye da shekaru goma da suka wuce.

Tana daya daga cikin kungiyoyi kusan 100 masu dauke da makamai da ke fafutukar ganin sun samu wurin zama a yankin mai arzikin ma’adanai, inda rikicin da aka dade ana fama da shi ya haifar da manyan matsalolin jin-kai a duniya.

Sai dai gwamnatin Rwanda ta musanta cewa tana goyon bayan ‘yan tawayen, amma a bara ta amince cewa tana da sojoji da na’urori makamai masu linzami a gabashin Congo domin kare tsaronta, lamarin da ke nuni da tarin dakarun Congo a kusa da kan iyaka.

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun kiyasta cewa akwai sojojin Rwanda har 4,000 a Congo.

Ma’aikatar harkokin wajen Congo ta fada a yammacin ranar Asabar cewa ta katse huldar diflomasiyya da Rwanda tare da fitar da dukkan jami’an diflomasiyya daga kasar nan take. Rwanda dai ba ta ce komai ba nan take.

Kwamitin Sulhu na MDD ya dage wani taron gaggawa kan tashin hankalin da ke kara kamari zuwa ranar Lahadi.

Congo ta bukaci a yi taron, wanda tun da farko aka shirya yi a gobe Litinin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG