Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Rwanda Da DRC Za Su Gana Akan Rikicin Goma.


Congolese civilians who fled from Goma, eastern Democratic Republic of Congo following gather at a reception center in Rugerero near Gisenyi, in Rubavu district, Rwanda, Jan. 28, 2025.
Congolese civilians who fled from Goma, eastern Democratic Republic of Congo following gather at a reception center in Rugerero near Gisenyi, in Rubavu district, Rwanda, Jan. 28, 2025.

Wani dan jarida da ke Goma, ya fada wa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa ana ci gaba da artabu a yankin tashar jirgin sama da ke birnin sannan ya ce da alamu fadan na dada ta’azara.

Shugaban Kenya William Ruto a ranar Litinin, ya ce shugabannin Rwanda da jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun amince su halarci wani taron da zai gudana yau Laraba don tattauna halin da ake ciki a gabashin kasar ta Congo inda ‘yan tawayen M23 suka ce ikirarin karbe birnin Goma wanda ke kan iyakar Congo da Rwanda.

“Duk mun amince da cewa, fiye da duk wani lokaci, yanzu, akwai bukatar mu yi Nazari akan abin da muke so mu cimma, ba don al’ummar gabashin Congo ba kawai, amma yankin baki daya,” abin da Ruto ya fada kenan a wurin wani taron manema labarai. Ya kara da cewa, “Abin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na bukatar hadin kan mu yanzu.”

Karbe Ikon Goma, birni mai yawan akalla mutane miliyan 2, ya haifar da fargabar yiwuwar ta’azarar rikicin da kuma raba mutane da muhallan su.

Wani dan jarida da ke Goma, ya fada wa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa ana ci gaba da artabu a yankin tashar jirgin sama dake birnin sannan ya ce da alamu fadan ya na dada ta’azzara. A sa’adda yake magana ta wayar tarho, wakiliyar Muryar amurca ta ji karar Harbin bindiga har ya katse wayar don ya nemi mafaka.

Tsawon shekaru, jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta yi ta zargin Rwanda da bai wa ‘yan tawayen M23 goyon baya, zargin da hukumomi a Kigali su ka musa.

Gwamnatin DRC ya fada a ranar Litinin cewa, dakarun gwamnatin Rwanda su na birnin Goma. Nan take jami’ai a Kigali ba su ce uffan ba game da wannan zargin.

Gwamnatin Congo “ta na ci gaba da kokarin kauce ma tashin hankali da asarar rayuka,” a cewar magana da yawun gwamnatin kasar Patrick Muyaya cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X. Muyaya y ace gwamnatin su tana shawartar mazauna Goma su zauna a cikin gidajen su sannan su guji kwasar ganima.

Mai magana da yawun ‘yan tawayen M23 Lawrence Kanyuka, ya fada ma VOA cewa, kungiyar tawayen ta karbe ikon birnin a karshen makon da ya gabata bayan wata zazzafar arangama da dakarun gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG