Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta Da Jami’an Tsaro A Sakkwato


Yan bindiga
Yan bindiga

Yayin da mahukunta ke kan daukar matakan dakile ayukkan 'yan bindiga a wasu sassa na Najeriya, su kuwa 'yan bindigar na kara kai farmaki ga al'ummomi musamman wadanda ke zaune a wurraren da ke fama da rashin tsaro.

A jiya Lahadi 'yan bindiga sun tun kari wasu garuruwa na gabashin Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, inda sukayi arangama da jami'an tsaro suka yi musayar wuta.

Da ma tun lokacin da gwamnatocin jihohin Katsina da Zamfara suka kaddamar da jami'an tsaro da zasu kare yankunan jihohin na su, aka yi hasashen 'yan bindiga zasu matsa zuwa jihohin da ba su samar da jami'an tsaron ba, su rika yin aika-aikar su.

Sai gashi ranar lahadi da marece an samu labarin tawagar 'yan bindiga sun tunkaro kauyukan Isa dake gabashin Sakkwato.

Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Isa, Hon Habibu Halilu Modaci, yace bayanai sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun taso ne daga Katsina suka hadu da na Zamfara suka shigo kauyukan gabashin Sakkwato, inda suka fafata da jami'an tsaro na sa kai suka yi musayar wuta.

Yace arangamar wadda aka fara misalin karfe biyar na marece zuwa har karfe takwas na dare an kashe 'yan bindiga da ba a san adadin su ba, kuma jami'an tsaron dake Isa suma sun samu raunuka.

Wakilin Muryar Amurka, Muhammad Nasir, ya zanta da wani mutumin Isa wada shi ma ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya kuma tuntubi rundunar 'yan sanda ta jiha akan wannan lamarin, sai dai ta bakin kakakinta, ASP Ahmad Rufa'i, tace tana da masaniya akan fafatawar da aka yi amma kakakin yace zai yi karin bayani daga baya, kuma kawo hada wannan rahoto ba a ji ba daga gareshi.

Gwamnatin jihar Sakkwato ma tamkar takwarorin ta na jihohin Katsina da Zamfara ta dauki jami'an tsaro da zasu kare yankunan, wadanda yanzu haka suna sansanin karbar horo suna samun horo.

A kan hakan ne mutanen yankunan da ke fama da matsalolin ke ganin idan sun kammala karbar horo akwai bukatar su yi aiki tare da takwarorinsu, duba da yadda dazukan da suka hada jihohin suna sarke da juna, kamar yadda dan majisar jiha na yankin Isa ke cewa.

Yanzu dai fatar jama'ar yankunan itace a samar da tsaron rayuka ta yadda jama'a zasu gudanar da lamuransu cikin lumana.

'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta Da Jami'an Tsaro A Sakwatto
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG