Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutum 22 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Abuja


Rundunar 'yan sanda
Rundunar 'yan sanda

An ceto akalla mutum 22 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga gundumar Dawaki da ke birnin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, kamar yadda ‘yan sanda da mazauna yankin suka bayyana a ranar Talata.

WASHINGTON D. C. - Matsalar Satar mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya yayin da gungun 'yan bindiga suke kai hari kan mutane a lungu da sako da manyan tituna da makarantu.

Yayin da aka rage samun ‘yan hare-hare da sace-sacen mutane a kewayen Abuja a ‘yan shekarun nan, lamarin dai ya zama ruwan dare a wajen birnin inda tsaro ya yake fuskantar tasgaro.

Wani mazaunin unguwar Nicholas Olayinka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Talata cewa da yawan ‘yan bindiga ne sanye da kakın soji ne suka mamaye sassan gundumar da misalin karfe 7:40 na yamma agogon kasar a ranar Litinin din da ta gabata, inda suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya haifar da fargaba yayin da jama’a suka yı ta tserewa don neman mafaka.

“A karshe dai mun gano cewa sun sace mutum kusan 19 a kan titunan da ke kewayen mahadar Fulani, da kuma wasu uku daga wani titin da ke makwabtaka da su,” in ji Olayinka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Josephine Adeh, a wata sanarwa da ta fitar, ta ce an samu rahoton faruwar lamarin daga wani mazaunin garin, inda daga nan ne aka tattara jami’ai tare da mafarautan yankin, suka kuma yi wa ‘yan bindigar kwanton bauna.

“Hakan ya kai ga mummunar musayar wuta inda aka ci karfin ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa da raunuka daban-daban, kuma an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su,” in ji Adeh.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG