Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama 'Yan bindigar Da Suka Kai Hari Kan Jirgin Kasa Na Kaduna


Gungun mutanen da 'yan sanda suka kama a jihar Kaduna (Facebook/Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna)
Gungun mutanen da 'yan sanda suka kama a jihar Kaduna (Facebook/Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna)

A watan Maris din 2022, ‘yan bindiga suka far wa jirgin yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin Najeriya.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta yi nasarar kama gungun ‘yan bindigar da ake zargi da kai hare-hare a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Yayin da take gabatar da wadanda ake zargin, rundunar ta ce daga cikin mutanen har da wadanda ake zargi da kai hari kan jirgin kasa da ya ta taso daga Abuja zuwa Kaduna a shekarar 2022.

Jirgin kasa na Najeriya
Jirgin kasa na Najeriya

A watan watan Maris din 2022, ‘yan bindiga suka far wa jirgin yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce mutum bakwai suka mutu daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin yayin da maharan suka yi garkuwa da mutane da dama.

Duk an sako mutanen bayan da suk kwashe watannin a hannun 'yan bindigar.

Sai dai jami’an tsaron sun ce hakarsu ta cimma ruwa bayan da suka kama wani gungun ‘yan bindigar a ayyukan sintiri da shawagin da jirgi mai saukar ungule ke yi a hanyar.

Makaman da aka karbe a hannun 'yan bindigar (Facebook/Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna)
Makaman da aka karbe a hannun 'yan bindigar (Facebook/Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna)

Daga cikin kamun da suka yi ‘yan sandan sun ce sun cafke wani Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da ‘Mande’ a daidai gadar sama da ke yankin Rido Junction.

“Wande ake zargin ya amsa cewa shi ne shugaban gungun masu garkuwa da mutane akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, wanda matsayinsa ya kai irin na Dogo Gide da Bello Turji.

“Ya sha sa hannu a garkuwa da ake yi da mutane ciki har da wanda aka sace dalibai a Jami'ar Green Field, sannan yana da hannu a kusan dukkan ayyukan garkuwa da mutane akan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.

Harsashan da 'yan sandan suka kama (Facebook/Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna)
Harsashan da 'yan sandan suka kama (Facebook/Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna)

“Kazalika wadanda ake zargin, sun amsa laifin cewa a ranar 28 ga watan Maris din shekarar 2022, Ibrahim da wani Auwal Ayuba da kuma wani Babangida Alhaji Bello suna daga maharan da suka kai hari kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja a tsakanin yankin Kateri-Rijina a jijar Kaduna.”

Sanarwar ta ‘yan sanda wacce suka wallafa a shafinsu na Facebook dauke da sa hannun kakakin rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ta ce.

Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda sun ce sun kama mutum 81 da ake zargi da fashi da makami, masu garkuwa da mutane 40, mutum 73 da ake zargi da kisa, 36 da ake zargi da ayyukan fyade, 22 da ake zargi da aikata muggan ayyuka.

Kazalika an kama makamai da dama a hannun ‘yan bindigar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG