Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Suka Sa Matsalar Rashin Tsaro Ke Karuwa A Abuja


'Yan sandan Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sandan Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Bayanai na nuni da cewa hakan na faruwa ne yayin da matsalar ta rashin tsaro ke raguwa a arewa maso yammcin kasar, kamar a yankunan jihar Sokoto.

Yayin da matsalar rashin tsaro ke kewaye babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, tare da jefa fargaba cikin zukatan jama'a mazauna yankunan, wasu jihohi da a can baya ke fama da matsalar mazaunan su sun ce yanzu suna samun sauki sannu a hankali.

Wannan kuma ba ya rasa nasaba ga yadda yanzu jami'an tsaro ke kutsa kai cikin dazuka suna fatattakar 'yan bindigar.

Wasu jihohi na arewacin Najeriya musamman yankin arewa maso yamma, a can baya sun kasance cikin halin lahaula saboda matsalar rashin tsaro inda kullum sai an samu rahoton kai hari a kashe ko a sace mutane.

Sai dai yanzu lamarin sannu a hankali ya fara sauyawa domin ana iya share mako biyu ba'a samun rahoton kai hari ba, kamar yadda wasu mazauna yankunan suka fadawa Muryar Amurka.

Bashir Altine Guyawa shugaban rundunar adalci ta Najeriya kuma dan asalin karamar hukumar Isa ta gabashin Sakkwato yankin da ya jima cikin wannan matsala ta rashin tsaro yana cikin wadanda suka tabbatar da haka.

Mazauna yankunan sun tabbatar da cewa yanzu suna ganin jami'an tsaro suna shiga dazuka suna fafatawa da 'yan bindiga, abin da wasu ke gani ba ya rasa nasaba da hadin kan da mahukunta ke samu yanzu wajen tunkarar matsalar, kamar yadda Farfesa Bello Bada shi ya tabbatarwa da Muryar Amurka.

Sai dai wani abu da za'a iya gani abin mamaki shi ne yadda yanzu 'yan bindigar ke kewayar babban birnin Najeriya Abuja, abin da ya sa har shugaban Najeriya ya gana da jami'an tsaro akan wannan matsalar.

Masana tsaro kamar, Dokta Yahuza Ahmad Getso, wanda ya jima yana sharhi da bayar da shawarwari akan tsaro a Najeriya, na ganin cewa rashin bin shawarwari da ake bayarwa a baya da kuma cin hanci na daga cikin abubuwan da suka kawo 'yan bindiga addabar Abuja.

Shi kuwa shugaban rundunar adalci Bashir Guyawa yana mai ganin cewa rashin kawar da manyan 'yan ta'adda kamar Baleri da ke dajin Kagara na daga cikin abubuwan da suka sa suke kewayar Abuja.

Mayar da himma wajen kawar da ayukkan 'yan bindigar ne kawai watakila kan iya tsirar da mahukunta daga zargin da wasu jama'a ke yi cewa ba da gaske ne suke yaki da ayukkan ta'addanci ba.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG