Kwamishinan ‘yan sandan Sikiru Akande ya tabbatar da kama wadanda ake zargi da aika laifuffukan daban daban yayin wani taron manema labarai a shedkwatar rundunar ‘yan sanda jihar.
Akande ya ce sun kama mutane 208 da suka aikata laifuffuka da suka hada da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, fashin daji da dai sauransu, kuma daga cikinsu tuni sun aike da 108 zuwa gaban kuliya domin fuskantar shari’a, sannan sun gabatar da 100 da ke hannunsu a gaban manema labarai.
Ya kuma kara da cewa sun yi nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda 7 da kuma wasu bindigogi kirar hannu da dama a ciki da wajen jihar.
A hirar shi da Muryar Amurka, Yakubu Ibrahim, daya daga cikin wadanda aka kama da zargin laifin garkuwa da mutane ya ce ya kirawo wani mutum da nufin zai yi garkuwa da shi in dai bai bashi wasu makudan kudade ba, kafin daga bisa ni kuma ‘yan sanda suka kama shi.
Shi kuwa Yusuf Muhammad mai shekaru 18 da haihuwa, yana daya daga cikin wadanda aka kama da manyan bindigogi kirar AK-47 guda hudu, wanda ya ce abokanansa ne daga Kamaru suka zo suka bashi ajiyar wadanda nan bindigogin.
A nasa bayani, wani mai suna Muhammad Musa, wanda rundunar ta kama yana yi wa ‘yan sandan jihar sojan gona ya bayyana cewa, yana daya daga cikin ‘yan kungiyar sa kai a jihar, inda daga bisani abun ya rike ya koma amfani da kayan ‘yan sandan jihar yana saka shinge yana kwacewa mutane kudi.
Ko a watan Disamban bara, rundunar ‘yan sanda jihar Adamawa ta yi nasarar kama mutane 108 da ake zargi da garkuwa da mutane da wasu sauran manyan laifuffuka.
Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Garba: