Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe 'Ya'yan Wani Pasto A Jihar Adamawa


Yan bindiga
Yan bindiga

Rundunar yan sandar jihar Adamawa ta tabbatar da cewa , wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan wani malamin addinin kirista suka kashe 'ya'yan malamin biyu su ka kuma arce da yar sa guda a yankin. Njanrin gada dake karamar hukumar Hong.

A hirar shi da Muryar Amurka, makwabcin limanin Kiristan Luka Yakubu ya bayyana cewa, ya dawo gida daga hira da misalin karfe goma na dare ne sai yaji ana ta harbi da bindiga a gidan Paston, da sai ya ji tsoro ya shiga daki don bashi da makamin da zai iya kare kansa ba. Bisa ga cewarsa, sun yi ta jira domin neman taimako daga jami'an tsaro amma har zuwa karfe biyu da wani abu basu samu agaji daga jami a tsaron yankin ba
A nasu bangaren, daya daga cikin jaurokan yankin Njanrin gada dake karamar hukumar Hong yayi ya bayyana yadda su ka sami gawawakin 'ya'yan Paston yayinda su ka tarar da Paston cikin jini shame shame. Nan take su ka yi kokarin kaisu asibiti anan aka tabbatar musu da mutuwa 'ya'yan.
Kakakin Rundunar yan sandar jihar Adamawa S P Sulaimani Yaya
Guroje ya tabbatar da aukuwar lamarin a zantawarsu da Muryar
Amurka a hetkwatar 'yan sandar jihar dake birnin Yola fadar jihar
Adamawa.
Saurari cikakken rahoton Salisu Lado cikin sauti:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG