Rundunar ta kuma gabatar da wasu masu garkuwan sama da goma, ta kwace kudi Naira miliyan hudu da sab'ain da uku da bindiga nan da a ke kira AK 147, da ma adduna da wukake daga hannunsu a cewar kakakin rundunar 'yan sandar jihar, SP Sulaimani Yaya Guroje.
Wani daga cikin masu garkuwa da mutanen da 'yan sandar suka kama mai suna Abdullhi Abubakar ya shaidawa Muryar Amurka cewa, sun yi garkuwa da wani yaro sun karbi miliyan hudu da dubu dari biyar amma an bashi dubu dari tara ne kawai a ciki.
A hirar shi da Muryar Amurka, Hassan Iro, wani mai garkuwan da mutane a jihar da 'yan sadan su ka kama da bindiga AK-147 a gidansa, ce sama da shekaru biyu kenan yana wannan aikin kuma sun dade suna daukan mutane suna karbar kudin fansa.
Saurari rahoton Salisu Lado a sauti: