Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Kara Samun Nasarar Murkushe Masu Garkuwa Da Mutane A Adamawa-'Yan Sanda


'Yan Sanda a Jihar Zamfara
'Yan Sanda a Jihar Zamfara

Rundunar ‘yan sandar jihar Adamawa ta yi nasarar kamo masu garkuwa da mutane da yawansu ya kai 87 da kuma babura guda uku da kudi Naira 58,500 a jihar, rundunar ta bayyana haka ne a taron manema labarai a helkwatan ‘yan sandan dake Yola babban binrnin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa C P Sikiru Akande shi ne ya tabbatar da hakan a wurin wani taron maneman labarai da suka gudanar a helkwatar jihar.

Wakilin Sashen Hausa ya yi nasarar zantawa da wasu masu garkuwan, Tukur Adamu na daya daga cikin masu garkuwa da mutane a jihar Adamawa wanda kuma rundunar ‘yan sandan ta kama.

Ya ce dama wani makocinsa ne suka yi ma barazanar duka in bai basu kudi Naira dubu dari biyar ba, shi kuma ya je ya yiwa ‘yan banga bayani su kuma suka kama shi suka bawa ‘yan sandar jihar.

Bashiru Adamu wani tubabben dan garkuwa da mutane ne wanda kuma ya sake komawa cikin aikin kuma ya shiga hannu ‘yan sanda.

Shima cewa ya yi rabon a yine ya sake jefa shi cikin wannan aikin ama ya gane kuskuren shi kuma da yardan Allah ba zai kara ba kuma wannan ya zama na karshe a wannan aikin.

Sai dai Haruna Auwal ya ce zarginsa da ake yi da wannan aikin na garkuwa da mutane yasa ‘yan sandar saka kamo shi amma shi baya cikin masu wannan aikin.

Ga dai rahoton Lado Salisu Muhammad Garba daga Adamawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG