Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Gurfanar Da Wasu Mutane 39 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Gurfanar Da Wasu Mutane 39 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Gurfanar Da Wasu Mutane 39 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gabatar da wasu da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane da kuma ‘yan fashin daji da yawansu ya kai talatin da tara a hedikwatar ‘yan sandan jihar.

ADAMAWA, NIGERIA - Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sikiru Akande, wanda Mataimakinsa ya wakilta, ya gabatar wa ‘yan jarida wadanda ake zargin. DCP Ajani Musibau ya yi jawabi wa manema labarai a babban ofishin ‘yan sandan na jihar adamawa.

Ajani ya yi jawabi ne akan wadanda ake zargin da cewa za a gurfanar dasu a gaban kotu domin a yi musu hukuncin da ya dace, ya kuma gode wa al'ummar jihar da suke bai wa ‘yan sandan goyon baya.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Gurfanar Da Wasu Mutane 39 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Gurfanar Da Wasu Mutane 39 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane

Wasu masu garkuwa da mutanen sun bayyana wa Muryan Amurka yadda suke yi da kudin fansar da suke karba a hannun mutane.

Buba Isuhu shugaban wasu masu garkuwa da mutane su shida, wadanda kuma dukansu ‘yan sandan jihar sun yi nasarar kamo su, ya yi karin haske akan yadda aka kamo su bayan sun karbi kudin fansa, amma ba su kashe ba.

Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Muhammad Garba:

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa Ta Gurfanar Da Wasu Mutane 39 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG