Rundunar sojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole dake aikin samar da tsaro tare da fafatawa da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar ta ce ta ceto mutane 3475 daga hannun 'yan ta'addan cikin watanni biyu kacal.
Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas shi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da rundunar ta kira a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
A cewarsa sun dukufa wajen tabbatar da kawo karshen kungiyar ta Boko Haram baki daya musamman ma a yankunan tafkin Chadi da dajin Sambisa inda ya ce sojojinsu sun bazu ciki. Bugu da kari sun hana 'yan kungiyar sakewa sakat.
A cikin watannin biyu sojojin rundunar sun samu kashe 'yan Boko Haram 166 sakamakon gumurzun da suka yi dasu. Baicin hakan sojojin sun kwato wasu motocin sojoji masu sulke, da motocin pick-up da makamai daga 'yan kungiyar. Inji kwamandan sojojin, sun kuma kame wasu 'yan Boko Haram 34.
Dangane da kakkabe 'yan kungiyar daga Sambisa Janar Nicholas ya ce da can da zara sojoji sun bar dajin sai 'yan Boko Haram su sake komawa ciki amma yanzu sun yanke shawarar kasancewa cikin dajin har sai sun gama dasu.
Kwamandan ya kara da cewa 'yan Boko Haram da dama sun mika kansu da kansu a kasashen Chadi da Kamaru da Nijar.
A saurari rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum