Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 40 A Karamar Hukumar Zurmi A Zamfara


Jana'iza A Jihar Zamfara
Jana'iza A Jihar Zamfara

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kashe sama da mutane arba’in, a wani sabon hari da suka kai a kauyen Birane dake cikin karamar hukumar Zurmi, a jihar Zamfara a Tarayyara Najeriya.

Lamarin ya faruwa da yammacin jiya Alhamis lokacin da wasu mutane kan Babura dauke da makamai suka kai hari tare da yin harbin kan mai uwa da wabi, a kauyen Birane inda suka kashe mutane da dama kana suka yi awan gaba da shanu.

Wasu majiyoyi sun ce, maharani sun tare wasu motoci, inda suka kashe tare da kona mutanen dake cikinsu da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwa kafin su shiga garin na Birane. Harin dai yayi kama da na ramuwar gayya, inji wani mazaunin garin zurmi wanda dansa yake cikin wadanda maharani suka harba amma bai mutu ba.

Da wakilin Muryar Amurka, ya tuntubi kwamishinan watsa labarai na Jihar, Muhammad Sanda Danjari, yace basu samu labari a hukumance ba, saboda sun ji labarin amma basu tabbatar da aukuwar lamarin ba.

Duk da yake ana ganin cewa ire-iren wadannan hare haren sun dan ragu a jihar ta Zamfara, yayin da yan bindigan suka karakata ga satar mutane da neman kudin fansa, amma lamarin na kokarin sake dawowa, domin a watan Nuwamba da ya gabata, an kai irin wannan hari a karamar hukumar Mulki ta Shinkafi, inda aka kashe mutane kusan ashirin da hudu tare da kona gidaje da dama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG