Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Yi Kuskure Da Kalmar Da Na Yi Amfani Da Ita-Biden


Trump da Biden
Trump da Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana jiya Litinin cewa, ya yi kuskure lokacin da ya gaya wa magoya bayansa cewa su “auna” abokin hamayyarsa Donald Trump a kokarinsa na jan hankali kan halayen abokin hamayyarsa, amma ya ce Trump yana yin amfani da kalamai masu tayar da hankali a kai a kai .

A hirar shi da ma’aikacin tashar talabijin ta NBC Laster Holt, Biden yace, "Kuskure ne yin amfani da kalmar, Ina nufin mayar da hankali a kai, mayar da hankali ga abin da yake yi,"

A ranar 8 ga watan Yuli, Biden, mai shekaru 81, ya yi jawabi ga wasu manyan masu ba da gudummawa a yakin neman zabensa, ya kuma ce suna bukatar su kauda hankalinsu a yakin neman zaben daga kanshi da kuma rashin taka rawar gani a mahawararsa da tsohon shugaba Trump, dan takarar Republican a zaben na ranar 5 ga Nuwamba.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Ya ce, "Ina da aiki daya kuma shine in doke Donald Trump ... Mun gama magana game da muhawarar. Lokaci ya yi da za mu sanya Trump a “gaba” in ji shi.

Wadansu 'yan jam'iyyar Republican sun yi watsi da wannan tsokaci yayin da suke zargin Biden da haifar da yanayin yunkurin kashe Trump a wani gangami a Pennsylvania ranar Asabar. Biden ya sha yin tir da tashin hankalin siyasa.

Shugaba Biden, ya yi kokarin ganin an maida hankalin kan abokin hamayyarsa, inda ya ambaci karairayin Trump, da kin amincewa da sakamakon zaben 2020 da Trump ya yi, da kuma rawar da ya taka a harin da aka kai a ranar 6 ga watan Janairun 2021 a babban birnin tarayya.

Zaben 2024
Zaben 2024

"Ni ba mutumin da ya ce ina son zama dan kama-karya tun daga ranar farko ba. Ba ni ne mutumin da ya ki amincewa da sakamakon zaben ba," in ji Biden.

Ya ce Trump ya na yin kalamai masu tada hankali, inda ya ba da misali da kalaman tsohon shugaban kasar kan zubar da jini da zai biyo baya idan ya fadi zaben 2024, da kuma yin dariya a lokacin da wani mai kutse ya kai wa Maigidan tsohuwar kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi, Paul hari da guduma a gidansu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG