Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS: Abin Da ‘Yan Nijar Ke Cewa Kan Kiran Da Gowon Ya Yi Na Dage Takunkumi


Tutocin kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali
Tutocin kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali

A watan Janairu kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suka sanar da shirinsu na ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.

Masana harkokin kasa da kasa a Nijar da yankunan Najeriya da ke makwabtaka da kasar ciki har da mabiya addinin Kirista, sun yi tsokaci kan yunkurin neman maslaha a kan takaddamar da ke tsakanin kungiyar ECOWAS da kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.

A watan Janairu kasashen uku suka ayyana shirinsu na ficewa daga kungiyar ta ECOWAS saboda abin da suka kira rashin bin ka’idojin da aka kafa kungiyar.

Kungiyar ta ECOWAS ta saka musu takunkumi saboda juyin mulki da sojoji suka yi a kasashen a lokuta daban-daban.

A farkon makon nan tsohon Shugaban mulkin soji a Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya yi kira da a dage takunkumin da aka sakawa kasashen, wadanda ke karkashin mulkin soji.

Kazalika ya nemi su ma kasashen su janye sanarwar da suka yi ta ficewa daga kungiyar.

A karshen wannan mako ne ake sa ran za'a gudanar da taro na musamman na shugabanin kasashen kungiyar ta ECOWAS, wanda ake ganin zai duba batun dage takunkumin.

AbdulRadjiku na Alhadji Musa mai inkiyar Shekarau, masanin harakokin kasa da kasa.

“Idan cikin tafiya ana samun shugabannin irinsu Janar Yakubu Gowon to komai na iya yi wu, duk abin da ake ganin ba za a iya daidaita shi za a iya daidatawa.” In AdbulRadjiku.

‘Yan Nijar da ke kan iyakokin kasashen biyu, sun bayyana ra'ayoyin su gameda da fatan da sukewa wannan taron na ECOWAS

“To gaskiya na ji dadi na yi fairn ciki, saboda babu abin da mu ke so illa Allah ya ba mu zaman lafiya.” In ji Muhammadu Mansur.

Haka zalika ‘yan Najeriya dake wannan yankin sun nuna farin cikin su da ma fatan su gameda tsoma bakin da Janar Yakubu Gowon ya yi a cikin wannan matsalar ta ECOWAS.

“Ai Nijar da Najeriya kamar Danjuma ne da Danjummai” In ji Bala Illela.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kiristocin cocin Angilika na Nijer ke taron zumunta maza a garin galmi a cikin jihar Tahoua, inda suka ce za suyi addu'o'i don ganin cewa kiran da tsohon shugaban kasar Najeriya Yakubu Gowon ya yi.

“Idan Yakubu Gowon ya fito ya yi wannan bayani, addu’o’i sun karbu, muna fada kullum da a yi addu’a” In ji Fasto Issufu Habu Kalo, Shugaban Zumunta maza ta kasa a Nijar.

Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:

ECOWAS: Abin Da ‘Yan Nijar Ke Cewa Kan Kiran Da Gowon Ya Yi Na Dage Takunkumi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG