Cikin 'yan gudun hijirar da kasar Nijar ta koro saboda rikicin mayakan Boko Haram da sojojinta a Difa akwai 140 'yan asalin jihar Neja da yanzu suka isa jiharsu.
Mutanen wadanda masu sana'ar kamun kifi ne a yankin Difa dake kasar Nijar 'yan asalin jihar Neja ne da sana'arsu ta kaisu yankin. Shugaban tawagar 'yan gudun hijirar Malam Abubakar Usman yace sun tafka asara mai yawa tare da ganin wahaloli irir-iri.
Yace sana'ar da suke yi ta tsaya. Wuraren da za'a ajiyesu kamar kananan hukumominsu suna bukatar taimakon gwamnati kama daga gwamnatin jiha zuwa ta tarayya.
Akwai mata da yara a cikin tawagar da yanzu suna zaune a sansanin alhazai. Wata Fati tace gaskiya sun sha wahala. Wai suna cikin kamun kifi aka ce an rufe hanya na tsawon watanni uku. Bayan watanni uku ba'a bude hanyar ba. Daga baya kuma sai aka fada masu cewa duk wani dan Najeriya ya fice daga kasar wanda kuma ya ki fita za'a koneshi da dukiyarshi.
Yanzu jami'an tsaro da hukumar bada agajin gaggawa ke tantance mutanen. Kuma tuni aka gano cewa 'yan asalolin kananan hukumomi bakwai ne dake cikin jihar ta Neja. Malam Garba Salihu jami'i a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja yace da suka kawosu sun duba lafiyarsu da ciyar dasu kafin su tantancesu domin gano kananan hukumominsu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
.