'Yan majalisar tare da ma'aikatan majalisar duk sun kasa shiga harabar majalisar saboda 'yansanda da suka rufe wurin suka kuma kewaye harabarta.
Yau kwanaki hudu ke nan da 'yansanda suka mamaye harabar majalisar. Akan wannan dambarwar mataimakin kakakin majalisar Onarebul Bello Agwara ya shaidawa manema labarai cewa zasu garzaya kotu domin kalubalantar 'yansandan. Yace tunda 'yansanda sun ce kotu ce ta basu damar rufe majalisar to su ma zasu garzaya kotun. Zasu gayawa kotun cewa abun da yansanda suke yi ya sabawa kundun tsarin milkin kasa da na majalisarsu.
A wani halin kuma gwamnan jihar Dr. Mu'azu Babangida Aliyu ya sheka zuwa kotu domin neman kotun da ta dakatar da 'yan majalisar daga duk wani yunkurin tsigeshi daga mukaminsa.
To amma Bello Agwara yace maganar tsige gwamnan abu mai sauki ne a wurinsu. Yace kowa nada 'yancin ya je kotu idan akwai abun da bai kwanta masa a zuciya ba. Wai domin kotu tace su dakata duk mai sauki ne amma duniya ta sa ido ta ga menene zai faru nan gaba.
Akan wai gwamnan yayi masu tayin nera miliyan goma kowannensu domin su sassauta maganar Onarebul Bello Agwara yace akwai ire-irensu a majalisar dake da akida. Ma'ana, ba za'a iya sayensu da kudi ba.
To saidai akwai bayanan dake cewa shugaban majalisar sarakunan jihar Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ya fara wani yunkurin shiga tsakanin gwamnan da 'yan majalisar dokokin domin kashe wutar da ta fara ruruwa.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.