NIAMEY, NIGER - ‘Yan Najeriyan sun yi kira ga wadanda suka sha kaye da su kasance masu halin dattako yayin da suka yi kira ga sabon zababben shugaban kasar muhimmancin hadin kan ‘yan kasa.
Galibin ‘yan Najeriya mazauna Nijar da suka bayyana ra’ayoyi a kan zaben kasar na 25 ga watan Fabrairu da ya gabata na cewa sun yi na’am da sakamakon da aka ayyana ‘dan takarar ta Jam’iya mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara a wannan fafatawa, duk kuwa da cewa ba haka wasu daga cikin su suka so ba da farko.
Haka kuma sun yi kira ga sauran bangarori da su kai zuciya nesa yayinda ya zama wajibi sabon zababben shugaban ya rungumi kowane ‘dan Najeriya don ci gaban kasa da jin dadin rayuwar talakawa injisu.
Miliyoyin ‘yan Najeriya ne ke zaune a Jamhuriyar Nijar shekara da shekaru inda suke gudanar da harakoki ba tare da wata matsala ba tamkar a gida, lamarin da ake alakantawa da babbar dangantakar iyaye da kankanni da ke tsakanin al’ummomin kasashen biyu masu iyaka guda, kamar yadda gwamnatocinsu ke ayyukan hadin guiwa a fannoni da dama don kara samar da walwala.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: