A shirye-shiryen tunkarar zanga-zangar gama-garin da aka tsara farawa a ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, gwamnatin tarayya ta ayyana ilahirin gidajen yari 256 dake fadin Najeriya a matsayin “wuraren da za’a tsaurara tsaro”, wadanda ba zata yarda a keta alfarmarsu ba.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin hukumar kula da gidajen yarin, Abubakar Umar tace, “duba da zanga-zangar gamagarin da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, hukumar kula da gidajen yarin Najeriya na sanar da al’umma cewa ta ayyana gidajen yarin kasar nan a matsayin wurare masu tsananin tsaro; don haka duk mutumin da bashi da wata harka da su ya yi nesa da su.”
Hukumar ta kuma jaddada cewa “gidajen yarin wasu cibiyoyin ne masu mahimmanci ga zaman lafiya da tsaron kasa.”
Sanarwa ta kara da cewa, “afkawa gidajen yarin na iya jawo rugujewar doka da oda, tare da sake jefa harkar tsaron al’umma cikin garari.”
Ta kara da cewar sakamakon shirin gudanar da zanga-zangar, an tsaurara tsaro a ilahirin gidajen yarin Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna