Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Masar Kalilan Suka Fito Kada Kuri'u a Zaben Majalisar Kasar


Wasu dake jiran su kada kuri'unsu jiya Lahadi a kasar Masar
Wasu dake jiran su kada kuri'unsu jiya Lahadi a kasar Masar

'Yan kasar Masar masu kada kuri’a kadan ne suka fito a jiya Lahadi don yin zabe kashin farko na ‘yan majalisu, wanda ake zaton zai kara karfafa mulkin Shugaban kasar Abdel Fattah El-sissi.

Za a ci gaba da zaben a yau Litinin a yankuna 14 daga cikin 27, wanda tun da safe za a bude runfunan zabe. Zaben da aka dade ana bata lokacin yinsa, zai cike gibin kujerun ‘yan majalisu guda 496.

Za’a ci gaba da zaben har ranakun 22 da 23 a wasu wuraren na cikin kasar. ‘Yan Kasar mazauna kasasehn waje tun a ranar Asabar suka fara kada kuri’unsu.

Ana zaton samun sakamakon zaben a farkon watan Disamba mai zuwa idan Allah ya kaimu. Kuma ba wani takamaiman labari daga jami'ai ko wata kafa ta fisbilillahi na fitowar jama’ar a jiya Lahadi, wanda aka yi hasashen ba zai wuce kashi 10 daga cikin dari ba.

Tun shekarar 2012 dai ba ‘yan majalisu a Misira, tun bayan da kotu ta soke zababbun ‘yan majalisun.

Yawanci a da ‘yan Muslim Brotherhood ne suka mamaye majalisar, jam’iyyar tsohon shugaba Masar Mohammed Morsi da aka haramtata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG